in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Lesotho ta kaddamar da aikin gina hanyar mota wanda Sin ta dauki nauyi
2018-12-07 10:53:42 cri

A jiya Alhamis aka gudanar da mashahurin bikin kaddamar da aikin gina titin mota na Mpiti zuwa Sehlaba-Thebe, wanda gwamnatin kasar Sin ta samar da rance kudin gudanar da aikin, bikin wanda aka gudanar a Qacha's Nek na kasar Lesotho.

Hanyar mai nisan kilomita 91 wanda ke yankuna masu tsaunuka. Za'a daga matsayin hanyar daga hanya mai kananan duwatsu zuwa titi mai santsi. Sakamakon wahalar aikin, za'a shafe watanni 36 gabanin kammala shi.

Aikin zai lashe kudi kimanin kudin kasar Maloti biliyan 1.8 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 128. Gwamnatin kasar Sin zata samar da rancen dala miliyan 100 domin gudanar da aikin.

Idan aikin ya kammala, zai samar da titi mai fadin mita 7 mai layuka biyu, zai rage nisan tafiya a mota daga Mpiti zuwa Sehlaba Tthebe daga tafiya sa'oi 4 zuwa tafiyar sa'a guda ko kuma sa'a guda da rabi. Aikin zai kuma bunkasa harkokin yawan bude ido kasancewar hanyar ta hade da babban filin shakatawa na Sehlaba-Thebe na kasar, wanda shi ne waje mafi shahara na tarihi a duniya dake kasar Lesotho.

Haka zalika aikin zai samar da guraben ayyukan yi sama da 300 ga al'ummomin yankin.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China