in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Afirka ta Kudu ya gana da jami'i mai kula da harkokin tuntubar kasashen waje na kwamitin tsakiyar JKS
2018-12-06 11:07:51 cri
Shugaban kasar Afirka ta Kudu, kana shugaban jam'iyyar ANC mai mulkin kasar ta Afirka ta Kudu Matamela Cyril Ramaphosa ya gana da jami'i mai kula da harkokin tuntubar kasashen waje na kwamitin tsakiyar Jam'iyyar Kwaminis ta Kasar Sin Song Tao.

A yayin ganawar tasu, Song Tao ya nuna yabo matuka kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da kuma jam'iyyun biyu, ya ce, kasar Sin tana son yin hadin gwiwa da kasar Afirka ta Kudu, domin aiwatar da ra'ayi daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma kansu, da kuma gudanar da sakamakon da aka cimma yadda ya kamata, a yayin taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka da aka yi a birnin Beijing, da kuma taron ganawar shugabannin kasashen BRICS a birnin Johannesburg. Sa'an nan kuma, ya kamata a zurfafa mu'amalar dake tsakanin jam'iyyun biyu, ta yadda za a karfafa dunkulewar kasashen Sin da Afirka bai daya.

A nasa bangaren, shugaba Ramaphosa ya ce, yana son ci gaba da karfafa dangantakar dake tsakanin jam'iyyun ANC da JKS, domin kiyaye moriyar kasashe masu tasowa cikin hadin gwiwa, da kuma nuna adawa ga tsarin kasuwanci na bin ra'ayin radin kai. Kuma yana fatan za a kara hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kasarsa bisa fannoni da dama domin tallafawa al'ummomin kasashen biyu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China