Kafofin yada labaru na kasar Afirka ta Kudu sun ruwaito a yau Jumma'a cewa, an ceto dukkan masu aikin hako ma'adinai kimanin dubu 1 wadanda suka makale a karkashin kasa a ranar 1 ga wata a mahakar Beatrix dake arewacin jihar Free sakamakon matsalar daukewar wutar lantarki da tsawa ta haddasa. (Tasallah Yuan)