in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi da Ramaphosa sun halarci bikin bude taron shawarwarin 'yan kimiyyar Sin da Afirka ta Kudu
2018-07-25 10:27:50 cri

Jiya Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Afirka ta Kudu Matamela Cyril Ramaphosa suka halarci bikin bude taron shawarwari a tsakanin masana a fannin ilmin kimiyya na Sin da Afirka ta Kudu.

A jawabinsa yayin bikin, Xi Jinping ya bayyana cewa, an samu ci gaba sosai ta fuskar hadin gwiwar fasahohi tsakanin kasar Sin da kasar Afirka ta Kudu, kuma kasashen duniya suna mai da hankali sosai kan ci gaban hadin gwiwar masanan Sin da Afirka ta Kudu a fannin kimiyya da fasaha, lamarin da ya karfafa dangantakar abokantaka tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare, wanda ya kuma kasance kyakkyawar dama ta raya hadin gwiwar kasashen biyu don cimma moriyar juna.

Haka kuma, Xi Jinping ya jaddada cewa, ya kamata mu gina sabon dandalin yin hadin gwiwa don neman ci gaba, zurfafa cudanyar dake tsakanin bangarorin biyu, karfafa tattaunawa tsakanin 'yan kimiyya matasa a sassan biyu, da kuma inganta hadin gwiwa da sauran kasashen duniya ba tare da rufa rufa ba, ta yadda za a ciyar da hadin gwiwar kimiyya da fasaha tsakanin Sin da Afirka ta kudu gaba yadda ya kamata.

A nasa bangare, shugaba Matamela Cyril Ramaphosa ya ce, an sami sakamako da dama a fannin kimiyya da fasaha bisa hadin gwiwar Sin da Afirka ta Kudu cikin 'yan shekarun nan. Kuma taron da za a yi ya nuna aniyarsu ta neman ci gaba ta hanyar sabunta fasahohi, da kuma karfi a asirce wajen hadin gwiwa a fannin tsakaninsu.

Gwamnatin kasar Afirka ta Kudu tana godiya matuka dangane da taimakon da kasar Sin take samar wa kasashen Afirka wajen neman bunkasuwa, kuma tana sa ran habaka hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka a fannin kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha bisa tsarin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China