Jiya Alhamis shugaba Jacob Zuma na kasar Afirka ta Kudu ya yi jawabi kan kasarsa a shekarar 2017.
A cikin wannan jawabi na shekara-shekara mafi muhimmanci a kasar ta Afirka ta Kudu, shugaba Zuma ya ambaci kasar Sin har sau uku, inda ya jinjinawa kyakkyawar huldar dake tsakanin kasarsa da Sin bisa manyan tsare-tsare, inda ya nanata cewa, kasar Sin tana daya daga cikin aminan Afirka ta Kudu mafi muhimmanci.
Afirka ta Kudu ta amince cewa, Gwamnatin Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin, gwamnati ce ta halal, kwaya daya tak da ke wakiltar kasar Sin, yana mai bayyana yankin Taiwan a matsayin wani bangare da ba za a iya raba shi daga babban yankin kasar Sin ba. (Tasallah Yuan)