in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kimanin masu hakar ma'adinai 900 ke makale a karkashin kasa a Afirka ta kudu
2018-02-02 12:20:56 cri
Gamayyar kungiyoyin kwadago a Afirka ta kudu(Cosatu) ta bayyana a jiya Alhamis cewa, kimanin masu aikin hako ma'adinai 900 ne suka makale a karkashin kasa a mahakar Beatrix dake arewacin jihar Free.

Shugaban kungiyar masu aikin hako ma'adinai da gine-gine (AMCU) Joseph Mathunjwa shi ne ya tabbatar da aukuwar lamarin. Ya ce matsalar daukewar wutar lantarki da ta faru sakamakon wata tsawa ce ta haddasa kimanin ma'aikata 940 dake aikin hako ma'adinan makalewa a karkashin kasa. Ko da yake an yi nasarar ceto 40 daga cikinsu, yayin da 900 ke can makale a karkashin kasa.

Kungiyar Cosatu dai ta bukaci gwamnati da ta gudanar da bincike don gano abin da ya haddasa wannan matsala. Mai magana da yawun gamayyar kungiyar ta kasa, Sizwe Pamla, ya jaddada cewa, akwai bukatar gwamnati da hada kai da bangarorin da abin ya shafa don bullo da managartan dokoki da za a rika amfani da su don tabbatar da kare lafiya da samar da matakan kariya da ma'aikatan hakar ma'adinan kansa ta yadda za a rage hadurran da ake gamuwa da su sanadiyyar aikin.

Bugu da kari, kungiyar ta yi kira da a samar da hidimomi na gaggauwa don inganta matakan da ake dauka na ceton ma'aikatan da ke makale a karkashin kasa.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China