in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadan Sin dake Afirka ta Kudu: Sin da Afirka sun raya shawarar ziri daya da hanya daya don samun moriyar juna da ci gaba tare
2018-11-24 17:03:22 cri
An gudanar da taron tattaunawa mai taken "Raya shawarar ziri daya da hanya daya a Afirka don samun moriyar juna da ci gaba tare" a jami'ar Witwatersrand dake kasar Afirka ta Kudu a jiya. Yayin taron, Jakadan Sin dake kasar Afirka ta Kudu Lin Songtian, ya ce an raya shawarar ziri daya da hanya daya don nuna goyon baya ga warware matsalolin rashin ayyukan more rayuwa da kwararru da kudade, da taimakawa kasashen Afirka wajen gaggauta bunkasa masana'antu da aikin gona.

Lin Songtian ya bayyana cewa, yanzu shawarar ziri daya da hanya daya ta kasance muhimmin dandalin hadin gwiwa da samun moriyar juna da ta shahara a duniya. Inda ya ce, shawarar ta mai da hankali ga bunkasar tattalin arziki, kuma ba ta shafi fannin siyasa ba. Kana ta tsaya tsayin daka kan manufar bude kofa da yin hadin gwiwa, ba aiwatar da ra'ayin ba da kariyar cinikayya ba. Haka kuma, ana aiwatar da shawarar ce don samun moriyar juna da ci gaba tare, ba nuna kiyayya ba tare da samun moriya ba.

Jakadan ya kara da cewa, Sin na goyon bayan raya kasar Afirka ta Kudu a matsayin kasa mai aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya bayan Habasha da Kenya, don amfanawa jama'ar kasashen biyu cikin hanzari.

A nasa bangaren, shugaban jami'ar Witwatersrand ya bayyana cewa, shawarar ziri daya da hanya daya tana da babbar ma'ana ga duniya baki daya, kuma bai kamata kasashen Afirka su ji tsoro ko nuna damuwa ga kasar Sin da ta samu moriya ta hanyar aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya ba. Ya ce, kamata ya yi su yi amfani da damar da shiga ajandar raya Sin da Afirka don neman samun ci gaba tare. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China