in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta kammala wa'adin aikinta na shugabancin kwamitin sulhu na MDD
2018-12-01 16:56:26 cri
Kasar Sin ta kammala wa'adin aikinta na shugabancin kwamitin sulhu na MDD, a jiya Juma'a.

A cikin watan Nuwanba, kwamitin ya kira taruka 35, inda aka zartas da kudure-kudure guda 6, yayin da aka fidda sanarwa guda 7, lamarin da ya nuna cewa, kasar Sin ta kammala wa'adin aikinta tare da cimma sakamako da dama.

A ranar 29 ga watan Nuwamba ne, zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Ma Zhaoxu, ya bayyana a taron manema labarai da aka yi a hedkwatar majalisar cewa, cikin wa'adin aikinta a matsayin shugabar kwamitin sulhu na MDD, kasar Sin ta shirya taruka da dama bisa taken "bunkasa sassa daban daban na MDD, domin kiyaye tsaro da zaman lafiyar duniya". Tarukan da suka ba da gudummawa wajen inganta zaman lafiyar duniya, da karfafa matsayin kasar Sin cikin harkokin kasa da kasa.

A sa'i daya kuma, kasar Sin ta sami yabo da karbuwa daga bangarori daban daban na kwamitin sulhun, bisa muhimman taruka biyu da ta kira, wadanda suka hada da "bunkasa sassa daban daban na MDD" da "karfafa ayyukan kiyaye zaman lafiya a kasashen Afirka". (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China