in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadan Kasar Sin a MDD ya bukaci kasashen duniya da su himmatu wajen cimma nasarar alakar moriyar juna
2018-10-10 20:08:00 cri

Jakadan kasar Sin a MDD Ma Zhaoxu ya yi kira ga daukacin kasashen duniya da su yi kokarin ganin sun yi nasarar cimma alakar moriyar juna, kana sun san cewa, kasancewar bangarori daban-daban shi ne kashin bayan samun ci gaba mai dorewa.

Ma ya kuma bayyana rashin jin dadinsa game da barazanar da dokar kasa da kasa kan harkokin cinikayyar duniya ke fuskanta, ya kuma shaidawa kwamiti na biyu ko kwamitin harkokin tattalin arziki da hada-hadar kudi na babban taron MDD cewa, ya kamata al'ummomin kasa da kasa su samar da yanayin kasuwancin da ya dace kamar yadda WTO ta tanada.

Jami'in na kasar Sin wanda ya alakanta kansa da kungiyar kasashen G77, ya bayyana cewa, ya kamata al'ummomin kasa da kasa su mayar da hankali ga batun kawar da talauci, samar da ilimi da kiwon lafiya.

Ya kara da cewa, muddin ana bukatar samun ci gaba mai dorewa, wajibi ne a samarwa kasashen dake yankin arewa maso kudu na kungiyar kasashen da tattalin arzikin su ke bunkasa da kungiyar kasashe masu tasowa isassun kudade gami da taimako.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China