A yau Alhamis ne mataimakiyar firaministan kasar Sin Sun Chunlan ta gana da babban sakataren hukumar kula da harkokin yawon shakatawa ta MDD Zurab Pololikashvili a nan birnin Beijing.
A jawabinta na maraba da zuwan Zurab kasar ta Sin, Sun Chunlan ta bayyana cewa, bangaren kasar Sin zai karfafa alaka da UNWTO a dukkan fannoni tare da zurfafa hadin gwiwar harkokin yawon shakatawa da hukumar karkashin shawarar ziri daya da hanya daya.
A nasa jawabin Zurab Pololikashvilli, ya yaba da dimbin nasarorin da kasar Sin ta cimma a fannin raya harkokin yawon shakatawa, yana mai cewa, hukumarsa za ta zurfafa tattaunawa da hadin gwiwa da kasar Sin, za kuma su hada gwiwa wajen bunkasa bangaren yawon shakatawa na duniya zuwa sabon matsayi.
Wannan dai ita ce ziyarar Zurab ta farko zuwa kasar Sin tun bayan da ya zama babban sakataren hukumar ta UNWTO.(Ibrahim)