Da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a wata hira da ya yi kwanan nan a lokacin bikin cika shekaru 20 da kafuwar kungiyar G77 reshen Vienna, Carlos A. Jativa, wanda kuma shi ne ke shugabantar kungiyar ta G77 reshen Vienna, ya ce, cigaban kungiyar al'amari ne mai matukar muhimmanci kasancewar tana wakiltar sama da kashi biyu bisa uku na al'ummar duniya baki daya.
Gudumowar da kasar Sin ke bayarwa yana da matukar muhimmanci, in ji shi.
A idon wannan wakili, bisa irin taimakon da kasar Sin take bayarwa, da irin bunkasuwar tattalin arzikin da take samu, da yawan tasirin da take da shi, da kuma irin abubuwan koyi da take bayarwa a bisa tarihi, ana kara samun cimma daidaito kan batutuwa da suka shafi cigaban kasashe masu tasowa a tsarin MDD.
Jativa ya yi amanna cewa, kasar Sin babbar mai taimakawa ce a bangarori uku da suka hada da nahiyar Afrika, Asiya da kuma Latin Amurka, musamman irin yadda take mayar da hankalinta wajen neman biyan muradun kasashen masu tasowa a zauren MDD. (Ahmad)