in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin kasar Sin ya yi kira da a rika girmama 'yancin kan kasa sama da albarkatu
2018-10-17 15:14:16 cri

Wakilin kasar Sin na dindindin a MDD Ma Zhaoxu, ya bukaci al'ummomin duniya su rika girmama 'yancin kan kasa sama da albarkatun dake kasashe daban-daban.

Ma ya yi kiran ne yayin muhawarar da kwamitin Sulhu na MDD ya tafka kan tushen dalilan dake haifar da rikice-rikice da rawar da albarkatun kasa ke takawa.

Ya ce ya zama wajibi a taimakawa kasashe amfana daga albarkatunsu da saukaka musu hanyoyin sarrafa su da baza komar tattalin arziki, ta yadda za su bi tafarkin da suke so na samun ci gaba mai dorewa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China