Fu Cong wanda ya bayyana hakan yayin da yake jawabi a taron kwamitin farko na babban taron MDD, ya ce tsarin kasancewar bangarori daban-daban shi ne mafi dacewa wajen warware duk wani kalubale da takaddama tsakanin kasashen duniya. Yana mai cewa, yanzu duniya na bukatar wannan tsari fiye da ko wane lokaci.
Jami'in na kasar Sin ya kara da cewa, wajibi ne kasashen duniya su martaba dokokin kasa da kasa kamar yadda bukatu da manufofin MDD suka tanada, a kokarin da ake na cimma ra'ayi guda, da samar da dauwamamman tsaro da warware bambance-bambance da takaddama ta hanyar shawarwari da tattaunawa, kana a martaba bukatun tsaron kowa ce kasa ta yadda daga karshe za a kai ga samun cikakken tsaro a duniya baki daya.(Ibrahim)