Lamido Moumouni ya bayyana haka ne jiya a birnin Yamai, fadar mulkin kasar, inda ya ce an sace 'yan matan ne a yankin Toumour na lardin Diffa.
Ya kara da cewa, gwamnatin kasar za ta dauki matakan gaggawa na neman 'yan matan, kuma mai yiyuwa za ta dauki matakan soja a wannan yanki.
Lardin Diffa yana kan iyakar Nijer da Nijeriya, kuma a 'yan shekarun baya-bayan nan, kungiyar Boko Haram ta kai hare-haren ta'addanci da dama a wannan lardi, wadanda suka haddasa mutuwar mutane da dama.
A daren ranar 21 ga wata, kungiyar Boko Haram ta kai hari kan wani kamfanin Faransa dake yankin Toumour dake lardin, harin da ya haddasa mutuwar a kalla guda 6, yayin da mutane 7 suka jikkata. (Maryam)