Gawarwakin 12 da aka tsinto suna da munanan raunuka a jikinsu, inji Kolo Babakura, shugaban jami'an tsaron sa kai na fararen hula.
Kolo yace, an kashe mutanen ne a lokacin da suke tsaka da gudanar da ayyuka a gonakinsu dake kauyen Kalle wadanda mayakan suka isa wajen a cikin manyan motoci biyu inda suka afkawa manoman, inda daga bisani maharan suka tsere cikin daji dake kusa da kauyen.
Babakura yace, akwai yiwuwar za'a iya samun karin wasu gawarwakin, kasancewar ana cigaba da bincike a kauyen.
Rundunar sojojin Najeriya ma ta tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa data fitar a jiya Asabar. Sai dai, rundunar sojojin tace gawarwakin mutane biyu kawai aka samu ya zuwa yanzu.
Ta kara da cewa, babu wani rahoton yin garkuwa da mutane da aka samu bayan kaddamar da harin.