Wata sanarwa da rundunar sojin Nijeriya ta fitar a jiya, ta ce rundunonin sojin biyu za su yi aiki tare wajen murkushe ragowar 'yan kungiyar Boko Haram dake iyakokinsu, musammam ta hanyar kaddamar da ayyukan soji na hadin gwiwa.
Sanarwar ta kara da cewa, dakarun kasashen biyu za su zage damtse ba tare da yin kasa a gwiwa ba, ga ayyukansu na kan iyakoki, wajen ganin sun dakile duk wasu ayyukan mayakan Boko Haram.
A baya, rundunonin biyu sun gudanar da ayyukan hadin gwiwa kan kungiyar Boko Haram a dajin Sambisa da yankin tafkin Chadi, inda kungiyar ke da manyan sansanonin horo. (Fa'iza Mustapha)