in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun Nijeriya sun kashe mayakan Boko haram akalla 3 yayin wata kwantar bauna da mayakan suka yi musu
2018-09-17 09:33:03 cri
Dakarun Nijeriya sun ci karfin mayakan kungiyar Boko Haram, inda suka kashe akalla 3 daga cikinsu, biyo bayan musayar wuta da suka yi a jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar.

Sanarwar da rundunar sojin kasar ta fitar a shafinta na Twitter, ta ce dakarun na briget ta 21 na aikin sintiri ne a lokacin da mayakan suka yi musu kwantar bauna, a kan titin Maiduguri zuwa Bama na jihar, inda ta ce an yi musayar wuta sosai tsakanin bangarorin biyu.

Hotunan da rundunar ta wallafa sun nuna an kashe akalla mayakan boko Haram 3, tare da kwato makamai da alburusai.

Sanarwar ta kara da cewa, har yanzu dakarun na aikin sintiri a yankin da nufin nemo mayakan da suka tsere da raunuka.

Ko a daren Larabar da ta gabata, an kashe mayakan Boko Haram da dama a garin Damasak dake jihar ta Borno, biyo bayan ba-ta-kashin da suka yi da sojoji. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China