in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun sojin Najeriya sun hallaka 'yan Boko Haram 14
2018-09-07 21:03:57 cri
Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarun ta sun hallaka mayakan kungiyar Boko Haram 14, tare da ceto wasu mutane 21 dake tsare a hannun mayakan, yayin wani samame a kauyen Pulka dake karamar hukumar Gwoza ta Jihar Borno a jiya Alhamis.

Kakakin rundunar dake yaki da 'yan Boko Haram a jihar ta Borno Texas Chukwu, ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Juma'ar nan. Mr. Chukwu ya ce sun samu nasarar ne sakamakon gaggauta daukar mataki da suka yi, bayan da suka samu labarin yunkurin mayakan na Boko Haram, na yiwa matafiya kwantan bauna, lamarin da ya sabbaba kona wata motar fasinja guda daya, tare da yin garkuwa da matafiyan dake wurin.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China