in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Najeriya sun kashe mayakan Boko Haram 14 tare da ceto mutane sama da 100 da suka yi garkuwa da su
2018-09-25 20:13:29 cri
Rahotanni daga Najeriya na cewa, sojojin kasar sun yi nasarar kashe mayakan Boko Haram 14, yayin wani samame da suka kaddamar da nufin kawar da gyauron kungiyar a yankin arewa maso gabashin kasar.

Mai magana da yawun rundunar sojan kasar Texas Chukwu wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, ya ce sojojin sun yi nasarar kubutar da mutane 146 daga hannun mayakan na Boko Haram, yayin wani farmaki da suka kai ranar Lahadi da kuma Litinin a yankin Gwoza dake arewacin jihar Borno. Sai dai kakakin ya tabbatar da cewa soja guda ya jikkata yayin kai harin.

Chukwu ya ce, yanzu haka ana tattara bayanan wadanda aka kubutar domin mika su ga hannun hukumomin da suka dace.

Koda a ranar 6 ga watan Satumban wannan shekara ma, sojojin sun yi nasarar kashe mayakan Boko Haram 14 a irin wannan samame da suka kaddamar a arewa maso gabashin kewayan Gwoza, aka kuma kubutar da mutane 21 da kungiyar ta Boko Haram ta yi garkuwa da su. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China