A wata sanarwar da kakakin rundunar sojin kasar Texas Chukwu ya fitar ta ce an yi musayar wutar ne a yayin da mayakan na Boko Haram suka yi yunkurin kaddamar da hari kan sansanin sojojin kasar da yammacin ranar Laraba a jahar Borno dake arewa maso gabashin Najeriyar.
An shafe sa'oi masu yawa ana fafatawa tsakanin bangarorin biyu, sai dai Chukwu bai bayyana takamammen adadin mayakan na Boko Haram da sojojin suka hallaka ba.
Irin salon dabarun yaki da kuma kwarewar aiki da dakarun Najeriyar suka nuna shi ne ya ba su nasarar samun galaba akan mayakan na Boko Haram. (Ahmad)