in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rasha za ta dauki matakai don neman daidaituwa idan Amurka ta janye jiki daga yarjejeniyar IRBM
2018-11-21 10:55:34 cri
Jiya Laraba, sakataren kula da harkokin labarai na shugaban kasar Rasha Dmitri Peskov ya bayyana cewa, idan kasar Amurka ta janye jikinta daga yarjejeniyar hana kera makamai masu linzami mai cin matsakaicin zango wato IRBM, hakan zai gurgunta yanayin daidaito bisa manyan tsare-tsare, kuma Rasha za ta dauki matakai domin mai da martani, da kuma kare yanayin daidaito tsakanin kasa da kasa bisa manyan tsare-tsare.

Haka kuma, ya ce, shugaban kasar Vladimir Putin ya jaddada a ranar 19 ga wata cewa, tabbas ne kasar Rasha za ta mai da martani, idan har kasar Amurka ta janye jikinta daga yarjejeniyar IRBM. A sa'i daya kuma, Dmitri Peskov ya bayyana cewa, kasar Rasha za ta dauki matakai domin kiyaye tsaro da moriyar kasarta, amma bai yi karin bayani game da irin matakan da za ta dauka ba. Ya ce, a halin yanzu, kasar Rasha tana son ci gaba da yin shawarwari da kasar Amurka kan batun yarjejeniyar IRBM.

A ranar 20 ga watan Oktoba, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar da cewa, kasarsa za ta janye jikinta daga yarjejeniyar IRBM, sabo da kasar Rasha ta saba da yarjejeniyar, kana yarjejeniyar ta hana Amurkan da ta raya sabon makamai. Sa'an nan, a ranar 24 ga wata, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya sanar da cewa, kasar Rasha za ta mai da martani ga kasar Amurka, da zarar ta janye jikinta daga wannan yarjejeniya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China