in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Trump ya ce babu wani shiri na doguwar tattaunawa tsakanin sa da shugaban Rasha a taron Paris
2018-11-08 11:00:12 cri

Shugaban Amurka Donald Trump, ya ce babu wani shiri na yin doguwar tattaunawa, tsakanin sa da takwaransa na Rasha Vladimir Putin, yayin taron cika shekaru 100 da kawo karshen yakin duniya na farko, wanda za a gudanar a birnin Paris na kasar Faransa a ranar Lahadi.

Trump ya bayyana hakan ne a jiya Laraba, yayin wani taron manema labarai da ya gudana a fadar White House. Ya ce yana sa ran cin abincin rana tare da shugaba Putin, tare da wasu sauran shugabannin kasashe, amma ba wata zantawa da aka shirya yi.

Shugaban na Amurka ya ce, za su sake haduwa da shugaban Rasha yayin taron kungiyar G20, kuma a wannan lokaci ne zai dan tattauna da shugaba Putin. Kaza lika Trump ya ce yana sa ran ganawa da shugaban Koriya ta arewa Kim Jong Un, a farkon shekara mai zuwa, sai dai ya ce Amurka ba ta gaggawa game da shirya ganawar, duba da yadda aka dage ganawar da aka shirya yi tsakanin wasu manyan wakilan kasashen biyu.

Gabanin kalaman na Shugaba Trump, fadar Kremlin ta Rasha, ta bayyana cewa, shugabannin Amurka da Rasha za su yi gajeriyar ganawa, yayin liyafar cin abincin rana a fadar Elysee, sa'an nan su sake yin cikakkiyar tattaunawa yayin taron kungiyar G20, wanda zai gudana a karshen watan nan a kasar Argentina.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China