Da yake ganawa da wani gidan talabijin na kasar Russia Today, Vladimir Putin, ya ce zancen gaskiya shi ne, suna kokarin kauracewa gudanar da atisayen soji a kusa da iyakar kasashe mambobin NATO, amma kuma, za su mayar da martani kan batun cikin lumana.
Kungiyar NATO, ta gudanar da babban atisayen sojinta na bana a Norway da kuma tekunan da suka kewaye ta, daga ranar 25 ga watan Oktoba zuwa 7 ga watan nan, atisaye mafi girma da ta yi tun bayan karshen yakin cacar baka.
Shugaba Putin ya ce yana fatan tattaunawa, wadda ita ake bukata a ko da yaushe, za ta yi kyakkywan tasiri kan yanayin.
Shugban ya kuma ce zai mara baya ga shawarar kafa rundunar kawance ta kasashen Turai don ta maye gurbin Kungiyar tsaro ta NATO. (Fa'iza Mustapha)