Cikin sanarwar, an bayyana cewa, cikin watanni 3 da rabi da suka gabata, sau 11 kasar Amurka na kara kakabawa kasar Rasha takunkumi. Sabo da kasar Amurka tana son matsa wa kasar Rasha lamba, ta yadda za ta hanawa Rashan 'yancin kai a harkokin kasa da kasa, to sai dai kuma takunkumin da kasar Amurka ke kakabawa kasar Rasha ba su da amfani.
A ranar 20 ga wata, kasar Amurka ta sanar da kakabawa wasu kamfanoni da mutane 9 na kasashen Iran da Rasha takunkumi, bisa zargin cewa, sun taba samar wa gwamnatin Syria man fetur. (Maryam)