in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Janyewar Amurka daga yarjejeniyar kawar da makami mai linzami mai cin matsakaicin zango za ta haddasa gasar kera makamai, in ji Rasha
2018-10-26 12:35:10 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha Maria Zakharova ta bayyana a jiya Alhamis cewa, mai yiwuwa ne, janyewar kasar Amurka daga yarjejeniyar kawar da makami mai linzami mai cin matsakaicin zango za ta iya haddasa gasar kera makamai a tsakanin yankuna daban daban na duniya.

A ranar 20 ga wata ne, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar da cewa, kasarsa za ta janye jiki daga yarjejeniyar kawar da makami mai linzami mai cin matsakaicin zango, bisa zargin da ya yiwa kasar Rasha cewa, Rasha ta hana kasar Amurka raya sabbin makamai cikin dogon lokacin da suka gabata. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China