in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakataren shugaban Rasha: Ba a kai ga sassauta dangantakar dake tsakanin Amurka da Rasha ba
2018-07-03 11:13:42 cri

Satataren watsa labarai na shugaban kasar Rasha Dmitri Peskov, ya bayyana daren jiya 2 ga wata cewa, ana farin ciki saboda ganin Amurka da Rasha sun kara tuntubar juna a siyasance, amma ba a kai ga sassauta yanayin tsamin dangantakar dake tsakaninsu ba tukuna.

Dmitri Peskov ya bayyana hakan ne, yayin da ya tabo batun ziyarar 'yan majalisar Amurka a kasar Rasha. An ce rukunin 'yan majalisar sun isa Rasha ne a ran 30 ga watan Yuni, kuma za su kasance a kasar har zuwa ranar 5 ga wannan wata na Yulin da muke ciki.

Cibiyar yada labarai ta TASS ta ba da labarin cewa, ziyarar ta wannan karo na da nasaba da halin da ake ciki game da shiryawa ganawa tsakanin shugabannin kasashen biyu.

Kaza lika Dmitri Peskov ya bayyana cewa, bai dace a tattauna batun samun sassauci tsakanin kasashen biyu ba, kasancewar akwai bambancin ra'ayi sosai tsakaninsu, amma shugabannin kasashen biyu na son yin shawarwari tsakaninsu bisa burin siyasa. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China