Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Ryabkov, ya bayyana a cikin sanarwa cewa, batun sayar da makamai ga Ukraine da kasar Amurka ta yi, ya canja daga aikin sirri zuwa aikin kasa a fili, wannan zai iya wargaza dangantakar dake tsakaninta da kasar Rasha.
Kana Ryabkov ya bayyana cewa, kasar Amurka ba ta kasance mai shiga-tsakani ba kan batun Ukraine, a maimakon hakan ta kasance mai taimakawa wajen ruruta wutar yaki.
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka ta sanar a ranar 22 ga wata cewa, ta tsaida kudurin samar da na'urori ga sojojin kasar Ukraine, kana ta ce wannan aiki ya taimakawa kasar Ukraine wajen kara karfin tabbatar da tsaron kasar, kasar Amurka ta nuna goyon baya da a zartas da yarjejeniyar Minsk wajen warware batun yankin gabashin kasar Ukraine. Bisa labarin da kafofin watsa labaru na kasar Amurka suka bayar, an ce, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya amince da sayarwa kasar Ukraine bindigogi samfurin M107A1 da darajarsu ta kai dala miliyan 41 da dubu 500. Ya zuwa yanzu, kasar Amurka ba ta sayar da manyan makamai ga kasar Ukraine ba. (Zainab)