Ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta gabatar da sanarwa a shafin internet cewa, Lavrov ya buga waya ga sakataren harkokin wajen kasar Amurka Rex Tillerson a wannan rana, inda suka yi musayar ra'ayoyi kan halin kasar Syria, kana sun tabbatar da kara hadin gwiwa wajen warware rikicin kasar Syria. Har wa yau kuma, Lavrov ya nuna ki amincewa da kasar Amurka ta kai hari ga dakaru masu goyon bayan gwamnatin kasar Syria, yana fatan Amurka za ta dauki matakai don magance sake faruwar irin wannan batu.
Sanarwar ta bayyana cewa, bangarorin biyu sun amince da yin amfani da matakan da ake dauka a yanzu ciki har da shawarwarin shimfida zaman lafiya na Astana da shawarwarin shimfida zaman lafiya na Genava don sa kaimi ga bangarori daban daban na kasar Syria da su yi sulhu da juna. (Zainab)