Fadar Kremlin ta Rasha ta ce Shugaban kasar Vladimir Putin ya kira shugaban Amurka Donald Trump ta wayar tarho, inda ya bayyana godiya ga hukumar leken asiri ta kasar wato CIA, bisa rahotannin da ta bayar da suka taimaka wajen dakile yunkurin ta'addanci a birnin St.Petersburg.
Hukumar tsaron Rasha ta ce a farkon makon da ya gabata, ta kama 'ya'yan kungiyar IS 7 da suka shirya kai hari kan fitaccen mujami'ar Kazan Cathedral na St.Petersburg, birni mafi girma a Rasha.
Fadar Kremlin ta ce bayanan da aka samu daga CIA, sun taimaka wajen aiwatar da bincike da tsare wadanda ake zargin.
Shugaba Putin ya shaidawa Donald Trump cewa, hukumomin tsaron Rasha ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen sanar da takwarorinsu na Amurka game da duk wata barazanar ta'addanci kan kasar da al'ummarta. (Fa'iza Mustapha)