Gwamnatin Rasha ta ce ta fara sanya karin haraji da kaso 25 zuwa 40 kan wasu kayayyakin Amurka dake shiga kasarta.
A watan da ya gabata ne Firaministan Rasha Dmitry Medvedev, ya rattaba hannu kan umarnin sanya sabon harajin, wanda zai fara aiki kwanaki 30 bayan wallafa shi a hukumance ranar 6 ga watanan nan.
Sabon harajin wanda martani ne ga karin harajin da Amurka ta yi na kaso 25 kan karafa da kuma kaso 10 kan samholo a ranar 23 ga watan Maris, ya shafi kayayyakin ginin titi da na masana'antar man fetur da iskar gas, da injunan sarrafa karafa da kuma kayayyakin fasahar sadarwa.
Ma'aikatar raya tattalin arziki ta Rasha ta ruwaito cewa, yawan sabon harajin a matakin da ake kai yanzu, zai kai dala miliyan 87.6 a shekara guda. (Fa'iza Mustapha)




