Cikin sharhin, shugaba Xi ya bayyana cewa, kasar Sin tana tsayawa tsayin daka kan ka'idar yin hadin gwiwa domin cimma moriyar juna, da kuma kara bude kofa ga waje. Kuma Sin tana maraba ga kasar Philippines da sauran kasashen duniya da su yi hadin gwiwa da ita wajen neman ci gaba cikin sauri. A nan gaba kuma, kasar Sin za ta ci gaba da yin hadin gwiwa da sassa daban daban, domin kiyaye tsarin cinikin dake tsakanin kasa da kasa bisa jagorancin kungiyar WTO, da kuma raya tsarin siyasa da tattalin arzikin duniya cikin yanayin adalci. (Maryam)