Da yake gabatar da jawabi ga taron shugabannin masana'antu da kasuwanci na APEC, wato kawancen kasashen Asiya da Fasifik kan tattalin arziki, a birnin Port Moresby na kasar Papua New Guinea, Xi Jinping ya ce bude kofa da hadin gwiwa ne kadai za su samar da karin damarmaki da ci gaba.
Ya yi kira da a kara kokarin kare tsarin cinikayya tsakanin kasa da kasa karkashin hukumar kula da cinikayya ta duniya WTO.
Har ila yau, ya ce yayin da ake tsaka da fuskantar sauye-sauye a duniya, bil adama na wani gaba na zabi tsakanin abubuwa masu muhimmanci.
Ya ce duniya na fuskantar sauye-sauyen da aka dade ba a gani ba. ya jadadda cewa muradun dukkan kasashe da makomar bil adama na tsakanin hadin gwiwa da kuma fito na fito da budewa da rufe kofa da kuma moriyar juna da kuma cin moriya daga gazawar wani bangare. (Fa'iza Mustapha)