A madadin gwamnatin kasar Sin da al'ummarta, Xi Jinping ya mika gaisuwa da fatan alkhairi ga gwamnatin Brunei da al'ummarta.
Shugaba Xi ya kuma jadadda cewa, kasar Sin da Brunei makotan juna ne kuma aminai, kana abokan hulda da suka aminta da juna, la'akari da daddadiyar huldar abota dake tsakaninsu.
Kasar ita ce waje na biyu da Shugaban Sin ya ziyarta a rangadin da yake a yankin Asiya da Fasifik. Da farko, ya kai ziyarar aiki kasar Papua New Guinea, inda ya gana da shugabanni daga kasashen tsibirin Fasifik dake da huldar jakadanci da kasar Sin, tare da halartar taron shugabannin Asiya da Fasifik kan harkokin tattalin arziki da masana'antu a Port Morseby, babban birnin kasar Papua New Guinea. (Fa'iza Mustapha)