in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya isa kasar Brunei don ziyarar aiki
2018-11-18 20:38:34 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya isa Seri Begawan don kaddamar da ziyarar aikinsa a kasar Brunei da ke kudu maso gabashin Asiya.

Xi Jinping ya jaddada cewa, Sin da Brunei makwabta ne,kuma aminai ne da suka aminta da juna. Tun bayan da aka kulla huldar diplomasiyya a tsakaninsu shekaru 27 da suka gabata, a ko da yaushe, kasashen biyu na zaman daidai wa daida, kana suna ta karfafa amincinsu a siyasance, baya ga yadda suka samu manyan sakamako wajen hadin kansu, wadanda suka kawo alfanu ga jama'ar kasashen biyu, da ma bayar da gudummawa ga zaman lafiya da wadatar shiyyar da suke ciki.

Xi ya kara da cewa, yana fatan ta ziyararsa a wannan karo, za a ci gaba da yada zumunta da ke tsakanin kasashen biyu, da tsara shirin da zai shafi ci gaban dangantakarsu, da ma kyautata dangantakar zuwa wani sabon matsayi, ta yadda za a kawo wa jama'ar kasashen biyu alheri sosai.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China