in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya isa Papua New Guinea domin fara ziyarar aiki da halartar taron APEC
2018-11-15 19:22:35 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya isa kasar Papua New Guinea a yau Alhamis, inda zai gudanar da ziyarar aiki, tare da halartar taron shugabanni game da tattalin arzikin kasashen yankin Asiya da tekun Fasifik ko APEC a takaice.

Wannan ce dai ziyarar farko da wani shugaban kasar Sin ya kai kasar, tun bayan da kasashen biyu suka kulla huldar diflomasiyya tsakanin su a shekarar 1976.

Yayin ziyarar da ya fara, shugaban zai kuma gana da shugabannin kasashen yankin 8, da suka kulla hulda da Sin a birnin Port Moresby, fadar mulkin Papua New Guinea.

Papua New Guinea ce zangon farko, a ziyarar da shugaban na Sin zai yi a wannan yanki, inda daga bisani zai ziyarci Brunei da kuma kasar Philippines.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China