in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da gwamnan Papua New Guinea
2018-11-16 16:17:54 cri
Yau Jumm'a, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da gwamnan kasar Papua New Guinea Bob Dadae a tashar jirgin ruwa ta Moresby.

A yayin ganawar tasu, shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, wannan shi ne karo na farko da ya kai ziyara kasar Papua New Guinea, kana karo na farko da shugaban kasar Sin ya ziyarci kasar. Bayan kasashen biyu sun kulla huldar diflomasiyya a shekarar 1976, sun ci gaba da habaka fannonin hadin gwiwar dake tsakaninsu, lamarin da ya zurfafa dangantakar abota dake tsakanin kasashen biyu. Haka kuma, kasar Sin za ta ci gaba da karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da tsibiran kasashen dake yankin Pacific.

A nasa bangare kuma, gwamna Bob Dadae ya ce, kasarsa tana maraba da zuwan shugaba Xi kwarai da gaske, kuma kasar Papua New Guinea ta kulla huldar diflomasiyya da kasar Sin bayan shekara daya da ta sami 'yancin kai, kana ziyarar shugaba Xi a kasar za ta daga dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi.

Bugu da kari, ya ce, kasar Papua New Guinea tana godiya matuka dangane da babban taimakon da kasar Sin ta baiwa kasar a fannonin ginin ababen more rayuwa, ba da ilmi da kuma kiwon lafiya da dai sauransu, kuma kasar Sin ta ba da babban goyon baya ga kasar wajen gudanar da kwarya-kwaryan taron shugabannin kungiyar hadin gwiwar tattalin arziki ta Asiya da Pacific ta APEC.

Kafin ganawar shugabannin biyu, Bob Dadae ya shirya wani babban bikin maraba da zuwa ga shugaba Xi Jinping a filin dake gaban babban ginin majalisar dokokin kasar. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China