in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Papua New Guinea sun amince da kulla huldar hadin gwiwa daga dukkanin fannoni
2018-11-16 19:18:05 cri
Kasar Sin da Papua New Guinea, sun amince da kulla huldar hadin gwiwa daga dukkanin fannoni tsakanin su. Hakan kuwa ya biyo bayan ganawar da shugaban kasar Sin Xi Jinping, da firaministan Papua New Guinea Peter O'Neill suka yi a Juma'ar nan.

Sassan biyu sun amince da hadin gwiwa, da martaba juna, da kokarin cimma moriyar juna, domin samar da ci gaban kasashen.

Yayin zantawar shugabannin biyu, sun jinjinawa dangantakar gargajiya tsakanin Sin da Papua New Guinea, sun kuma tattauna game da hanyoyin bunkasa dangantakar dake tsakanin kasashen.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China