Shugaba Xi wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban hukumar zartawar rundunar sojojin kasar, kuma shugaban kwamitin koli game da zurfafa gyare gyare daga dukkanin fannoni na kasar, ya yi kira da a kara azama, wajen yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, da kokarin cimma manyan nasarori a fannin ingantawa, da bunkasa tsarin mulkin gurguzu mai halayyar musamman na Sin, da zamanantar da salon aiwatar da manufofin gwamnatin kasar.
Kaza lika ya bukaci sassan masu ruwa da tsaki, da su kara zage damtse wajen aiwatar da gyare-gyare, da kara bude kofa a sabon zamani da ake ciki.