Shugaba Xi ya ce, sararin samaniya babban arziki ne na dukkanin bil Adama, yin nazari, habaka da kuma yin amfani da sararin samaniya cikin zaman lafiya su ne babban burin bil Adama. Kasar Sin tana fatan kasashen duniya za su yi hadin gwiwa domin karfafa dunkulewar bil Adama, da zurfafa mu'amalar kasa da kasa kan harkokin sararin samaniya, bisa ka'idojin nuna adalci, da fahimtar juna, da kuma yin amfani da harkoki cikin zaman lafiya.
Haka kuma, kasar Sin tana tsaya tsayin daka wajen habaka da yin amfani da harkokin sararin samaniya, da kuma kare yanayin sararin samaniya yadda ya kamata, domin raya fasahohin sararin samaniya ta yadda hakan zai taimakawa daukacin bil Adama. (Maryam)