Shugaba Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin koli na JKS, kuma shugaban hukumar zartaswar rundunar sojojin kasar, ya halarci wani muhimmin baje kolin nune nune, wanda aka shirya domin murnar cika shekaru 40 da fara aiwatar da manufar gyare gyare a gida, da bude kofa ga kasashen waje.
Ya kuma bayyana cewa, baje kolin zai taimaka wajen cimma daidaito, da karfafa gwiwar juna, tare da bunkasa hadin kai, da zaburar da karin ci gaban kasa.
A Talatar ne aka bude baje kolin nune nune, game da manufofin kasar Sin na aiwatar da gyare-gyare a gida, da bude kofa ga kasashen waje a nan birnin Beijing, domin murnar cika shekaru 40 da aiwatar da manufofin.
Yayin baje kolin an gabatar da hotuna, da rubatattun bayanai, da faya fayen bidiyo, da ayyukan cudanya da baki mahalarta da sauransu, domin nuna irin matakai da kasar Sin ta bi wajen kaiwa ga gagarumin ci gaban ta na yanzu, da wanda take fatan samu nan gaba.
Kimanin mutane 1,000 ne dai suka halarci bikin bude baje kolin.