Shugaba Xi ya yi wannan tsokaci ne a Litinin din nan, yayin da yake zantawa da wakilan yankunan biyu. Ya ce yana da burin ganin 'yan uwa na yankunan biyu sun shiga adama da su, wajen aiwatar da wadannan manufofi masu fa'ida, da sahihiyar zuciya da kishin kasa, ta yadda hakan zai fadada ci gaban yankunan na musamman, tare da taka tasu rawa, wajen kara farfadowar kasar Sin baki daya.
Wakilan yankunan nan Hong Kong da Macau, sun ziyarci birnin Beijing, babban birnin kasar ne domin murnar cika shekaru 40, da fara aiwatar da manufar gudanar da gyare gyare a gida, da bude kofa ga kasashen waje ta kasar.