Gao Feng ya kara da cewa, daga ranar 1 zuwa ranar 11 ga watan Nuwanba, adadin hajojin ketare da aka sayar ta intanet ya wuce yuan biliyan 30, kuma kasashen Japan, Amurka, Koriya ta Kudu, Australia da kuma Jamus, su ne ke kan gaba cikin jerin kasashen da aka fi shigo da hajojinsu daga ketare. Wani babban kamfanin sayar da kayayyaki na intanet na kasar Sin, ya shigo da hajoji daga kamfanonin ketare kimanin dubu 19, daga kasashe da kuma yankunan ketare 75. A sa'i daya kuma, masu sayayya na kasashen ketare sama da miliyan biyu sun kashe yuan biliyan 3 don yin sayayya a kamfanonin cinikayya na intanet na kasar Sin. (Maryam)