Mr. Yang Jiechi, ya bayyana hakan ne a jiya Juma'a, yayin taron manema labarai da ya gudana, bayan kammala taro na biyu, na wakilan Sin da Amurka game da harkokin diflomasiyya da tsaron kasashen.
Ya ce ya dace Sin da Amurka su fadada tattaunawa, tare da ci gaba da cudanya, da wanzar da shirye shirye, na tabbatar da nasarar ganawar shugabannin.
Mr. Yang, da sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, da sakataren tsaron Amurka James Mattis ne suka jagoranci taron. Kaza lika taron ya samu halartar dan majalissar zartaswar Sin, kuma ministan tsaron kasar Wei Fenghe. (Saminu)