Ma Zhaoxu, ya bayyana hake ne jiya, yayin muhawarar da aka yi a zauren kwamitin sulhu na MDD.
Wakilin na kasar Sin ya bayyana cewa, karfafa dangantakar kasa da kasa da nauyin MDD, matsaya ce guda ta al'ummomin kasa da kasa, wadda Sakatare Janar na majalisar Antonio Guterres da shugabar zauren majalisar Maria Fernanda Espinosa Garces da sauran kasashe mambobin majalisar, suka bayyana goyon bayansu gareta, yayin zaman babban zauren majalsar da aka yi cikin watan Satumban bana.
Ya kuma jadadda kudurin kasar Sin na kare dokoki da karfafa dangantakar kasa da kasa, yana mai alkawarin cewa, a shirye kasar Sin ta ke ta hada hannu da dukkan kasashe wajen gina al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil adama da samar da duniya mai cike da zaman lafiya da ingantacciyar rayuwa ga kowa. (Fa'iza Mustapha)