in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta daddale yarjejeniyar kera babban jirgin ruwan yawon shakatawa ta farko
2018-11-13 15:33:44 cri
Yayin taron tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakanin kamfanonin mallakar kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin da kamfanonin kasa da kasa da aka gudanar a kwanakin baya, babban kamfanin kera jiragen ruwa na kasar Sin wato CSSC a takaice ya daddale yarjejeniyar kera manyan jiragen ruwan yawon shakatawa mai samfurin Vista guda 6 da adadin nauyinsu ya kai ton dubu 135 tare da kamfanonin Amurka da Italiya.

An ce, wannan ne karo na farko da Sin ta daddale yarjejeniyar kera babban jirgin ruwan yawon shakatawa, wannan alama ce dake cewa, babban kamfanin kera jiragen ruwa na Sin ya fara gudanar da aikin kera manyan jiragen ruwan yawon shakatawa a hukunce, wanda zai sa kaimi ga inganta sha'anin masana'antun kera jiragen ruwa na kasar Sin.

An ce, tsawon jirgin ruwan yawon shakatawar da za a kera bisa yarjejeniyar zai kai mita 323.6, kana fadinsa zai kai mita 37.2, yayin da tsayinsa zai kai mita 72.2. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China