in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin IBTC ya bullo da cibiyar hada-hadar kudi tsakanin Afirka da Sin
2018-11-15 09:22:25 cri

Bankin Stanbic IBTC ya kaddamar da wata cibiyar hada-hadar kudi da nufin saukaka mu'amalar kudade tsakanin 'yan kasuwan kasar Sin dake harkokin kasuwanci a Najeriya da kuma kamfanonin Najeriya dake harkokin cinikayya a kasar Sin.

Da yake karin haske yayin kaddamar da cibiyar da ya gudana a yankin Ilupeju dake Legas cibiyar kasuwancin kasar, babban jami'in rukunin bankin na IBTC Yinka Sanni, ya ce, cibiyar wata kafa ce ta gudanar da duk wasu harkokin na kudade kai tsaye tsakanin Najeriya da kasar Sin.

Bugu da kari, cibiyar za ta yi kokarin hade abokan huldar kasashen biyu da tsarin banki na zamani na kasar Sin ta yadda kasashen za su rika mu'amalar kudade ba tare da wata matsala ba.

Cibiyar ta kuma tanadi ma'aikata da suka kware a fannin Sinanci da al'adun Sinawa, za kuma ta rika tattaunawa da ba da shawarwari na hidima ta wayar tarho, da yanar gizo ko adireshin E-mail ga abokan huldarta Sinawa da 'yan Najeriya. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China