Rahoton ya kara da cewa, idan kasar Amurka ta ci gaba da yake-yaken da take yi a kasashen Afghanistan, Syria da kuma Iraqi, adadin kudin da za ta kashe a fannonin ba da jinya ga tsoffin sojoji, da biyan kudin ruwa na basassun da ta ci zai karu, kana, bisa hasashen da aka yi, ya zuwa kasafin kudin shekarar 2023, yawan kudin da kasar za ta kashe zai karu da dalar Amurka biliyan 808. (Maryam)