Donald Trump ya wallafa a shafinsa na Tweeter a jiya cewa, yana fatan Saudiyya da OPEC ba za su rage samar da mai ba, kuma kamata ya yi farashin mai ya yi kasa bisa yadda ake samarwa.
Hukumar kula da makamashi ta Amurka, ta bayyana a watan da ya gabata cewa, dawo da takunkumai kan Iran da Amurka ta yi, zai kara haifar da rashin tabbas kan farashin man fetur, kuma tasirin takunkuman zai karu a nan kusa.
Daga bisani ne kuma, OPEC ta ce kasashe mambobinta, sun shiryawa cimma bukatun kasuwar mai ta duniya, ko da za a samu karancin mai saboda dalilai na siyasa, sannan za su ci gaba da kokarin tabbatar da daidaito a kasuwar mai.
Dangantakar Amurka da Saudiyya ta dan samu tangarda a baya bayan nan, sanadiyyar yawan mutanen da hare-haren da Saudiyyar ke jagoranta ya rutsa da su a Yemen da kuma kisan dan jaridar kasar Jamal Khashoggi a Turkiyya. (Fa'iza Msutapha)