in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na fatan Amurka za ta cika alkawarinta na girmama zabin kasashe daban daban
2018-11-14 20:21:46 cri
Kwanan baya mataimakin shugaban kasar Amurka Mike Pence, ya ce kasarsa na fatan duk kasashen dake yankin tekun Indian da Pasific, za su iya zaben hanyoyinsu cikin 'yanci, da kuma neman moriyarsu, kuma babu wanda zai iya bin ra'ayin mulkin mulaka'u ko kai hari a yankin.

Game da haka, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin madam Hua Chunying, ta ce tana fatan Amurka za ta kai ga cika wannan alkawari. Hua ta bayyana hakan ne, a yayin taron manema labaru da aka shirya a yau Laraba, inda ta ce, har kullum kasar Sin na ganin cewa, ya kamata kasa da kasa su girmama juna game da mulkin kai, da cikakken yankin kasa, da rashin kai wa juna hari, da rashin tsoma baki cikin harkokin gida na juna. Kaza lika kasashe daban daban, na da ikon zaben hanyoyin ci gaba dake dacewa da halin da suka samu kansu a ciki, hakan kuma muhimmin abu ne dake cikin ka'idoji guda biyar, na zaman tare cikin lumana. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China