in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta yi barazanar rage tallafin ta ga asusun wanzar da zaman lafiya na MDD
2018-11-10 16:07:04 cri
A jiya Juma'a ne kasar Amurka, ta ayyana barazanar rage tallafin da take bayarwa, ga asusun wanzar da zaman lafiya na MDD tun daga wata mai zuwa, tana mai cewa Amurka ba ta daukar tallafin na ta a matsayin sadaka.

Da take tsokaci game da hakan, yayin zaman mahawarar da kwamitin tsaron MDD ya gudanar a jiya Juma'a, wakiliyar dindindin ta Amurka a MDD Nikki Haley, ta ce Amurka ce ke samar da kaso 25 bisa dari, na kudaden da ake kashewa a ayyukan wanzar da zaman lafiya wanda hakan ya sabawa adalci, kasancewar Amurkan ba ta dauki tallafin da take samarwa a matsayin wani nau'i na sadaka ba.

Sai dai a nasa tsokaci, wakilin dindindin na kasar Rasha a MDDr Vassily Nebenzia, cewa ya yi wasu kasashe, na kokarin bunkasa tasirin su a duniya ta hanyar yin babakere. Ya ce a zahiri irin wadannan kasashe na nuna amincewa da tsarin cudayyar kasashen daban daban, amma a asirce ba sa goyon bayan hakan, sai fa idan hakan zai dace da wasu sharudda na kashin kan su.

Da yawa daga masharhanta dai na ganin Amurka, na daukar matakai ne dake alamta burin kasar, na janyewa daga harkokin cudanyar kasa da kasa. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China